16 Yuli 2026 - 17:30
Source: ABNA24
Kafofin Larabawa: Iran Ta Kai Hari Mafi Muni A Bahrain

A cewar majiyoyi, an ji karar fashe-fashe da dama a Bahrain. An kuma sami fashe-fashe masu ƙarfi a sansanonin soji na Amurka a Jordan. Rahotanni sun nuna cewa, bayan waɗannan abubuwan, an ƙarfafa tsaro a yankin kuma an ƙara ayyukan soji na Amurka.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Majiyoyin labarai na Larabawa sun yi iƙirarin cewa, harin da aka kai a kan sansanonin soji na Amurka a Bahrain, shi ne hari mafi faɗi da aka taɓa yi a yayin ci gaba da rikici. A cewar kafofin yada labarai na gida, an kai harin ta sama a kan sansanin sojojin Amurka da ke Bahrain, tare da jin karar ƙararrawar faɗakarwa a Bahrain.

A cewar sashin hulda da jama'a na IRGC, 'yan mintuna da suka gabata, an gano kuma aka harbo wani jirgin mara matuki na MQ-9 na makiya a sararin Andimeshk, wannan aiki wata muhimmiyar nasara ce ga ƙarfin tsaron saman zamani na Iran da kuma tabbatar da tsaron sararin samaniyar ƙasar.

Majiyoyin soji na Iran sun ce, Idan Amurka da kawayenta suka ci gaba da matsin lamba ko hare-hare a kan Iran, to IRGC da sojojin Iran za su ci gaba da ayyukansu na ramuwar gayya masu tsanani da faɗi, za su yi amfani da dukkan ƙarfin soji don kare tsaro da ikon mallakar ƙasar.

…………………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha